OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jam'iyyar Labour Ta Tsayar Da Peter Obi a Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa

Jam'iyyar Labour Ta Tsayar Da Peter Obi a Matsayin Dan Takar

Peter Obi| Photo Source: Daily Post

A yau (Litinin) ne jam’iyyar Labour (LP) ta zabi tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Zaben dai ya baiwa Obi nasara bayan da Farfesa Pat Utomi ya sauka masa.

Obi ya kasance dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Ya kuma kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kwanan nan kafin ya fice daga jam’iyyar zuwa LP.

Da yake jawabi ga wakilai a babban taron jam’iyyar na kasa a jihar Delta, Farfesa Pat Utomi ya bayyana cewa Obi zai yiwa kasa hidima a matsayin shugabanta.

Ya kuma bayyana cewa Obi na da dukkan kwarewar da ake bukata domin ciyar da kasar nan zuwa ga tudun mun tsira.

Ya kuma yi alkawarin hada kan Wasu jam’iyyu domin tabbatar da nasarar jam’iyyar tasu a zaben 2023.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci