OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hamzat ya gargadi magoya bayan jam’iyyar Labour party a kan labarun kanzon kurege a Legas

Hamzat ya gargadi magoya bayan jam’iyyar Labour party a ka

Mataimakin gwamnan jihar Legas, Obafemi Hamzat, ya gargadi 'yan bani na iyan siyasa da magoya bayan jam’iyyar Labour da su kaurace wa labarun karya da ba za su haifar da wata riba a siyasa ba.

Mista Hamzat ya yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Tunde Alao, ya fitar ranar Lahadi a Legas.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, hoton wani mutumi ya bayyana a yanar gizo in da aka bayyana cewa: "Dan Mataimakin Gwamnan Jihar Legas, Femi Hamzat, ya bi sahun magoya bayan Peter Obi".

 Hotunan sun bazu a kafafen sada zumunta ranar Asabar bayan an gudanar da yawon kamfen a jihar Lagos.

A cewar sanarwar, mutumin da ke cikin hoton "ba dan mataimakin gwamna kuma ba danginsa ba.

“Wannan jita-jitan ya kasance wani yunkuri ne na batanci, karya dan haifar da rikici tsakanin mataimakin gwamna da masoyansa da sauran mabiyan sa a fadin kasar nan.

“Dr Hamzat ya yi kaurin suna wajen sadaukarwa da biyayya ga gwamnatin Sanwo-Olu  na jihar Lagos da jam’iyyar All Progressives Congress.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci