OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Sama Da Naira Miliyan 300 Ga Malaman Jami'a

ASUU: Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Sama Da Naira Miliya

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta amince da biyan Naira miliyan 304 a matsayin alawus-alawus ga ma’aikatan jami’ar Yusuf Maitama Sule.

Kwamishinan yaɗa labarai, Muhammad Garba ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Juma’a.

Ya ce majalisar zartaswar jihar ta amince da biyan kudin bayan la’akari da roƙon da gwamnati ta yi wa ma’aikatan na su koma azuzuwa, wanda zai fara aiki daga Oktoba, 2022.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa taron da gwamnatin jihar Kano ta yi da wakilan kungiyar ASUU a baya daga jami’o’in gwamnatin jihar biyu a farkon makon ya ci tura.

Garba ya bayyana yadda kason zai kasance kamar haka Naira miliyan 297.6 na ma’aikatan da aka tantance, yayin da aka kiyasta Naira miliyan 6.5 na sauran ma’aikatan ilimi 10.

Kamar yadda ya bayyana cewa majalisar ta kuma amincewa da sakin Naira miliyan 82.1 ga wannan jami’a domin samar da kayan aiki ga tsangayar Kimiyya.

A halin da ake ciki, malaman makarantar har yanzu ba su ce komai  akan tayin da gwamnatin tayi ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci