OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ina Mamakin Irin Tabar Da Fadar Shugaban Ƙasa Suke Sha, Cewar Ortom

Ina Mamakin Irin Tabar Da Fadar Shugaban Ƙasa Suke Sha, Cew

Samuel Ortom

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya caccaki babban mataimaki na shugaban kasa a harkan yaɗa labarai, Mallam Garba Shehu, biyo bayan kalaman da gwamnan ya akan rashin tsaro a kasar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, a martanin da Gwamna Ortom ya bayyana cewa wasu manyan jami’an soji, sun shaida masa cewa, shugaba Buhari ya gargade su da su dakile hare-haren da ake kai wa makiyaya.

Yayin da Garba Shehu ya ce Ortom “yana tsammanin za'a yarda cewa manyan jami’an tsaron Najeriya za su faɗa masa bayanin sirri akan tsari? Don a bayyane, baza su yi ba. "

Da yake mayar da martani ga kalaman mai magana da yawun shugaban kasa, babban mataimaki na musamman a harkan yaɗa labarai ga gwamna Ortom, Raymond Magen ya ce ‘yan Najeriya masu kishin kasa sun san gwamnan a matsayin mutumin da ba ya yin kalamai marasa tushe a kan wasu muhimman batutuwa.

A cikin wata sanarwa, Magen ya ce akan tsaro a  lokuta da yawa, suna yi,  Kamar gwamnan jihar da ke fama da hare-haren makiyaya, ba abin damuwa ba ne, dole ne ya samu bayanai daga dukkan jami’an tsaro da ke da hannu wajen kai hare-haren makiyaya.

“Yayin da Shehu yace idan da gaske Gwamna Ortom na fadin gaskiya, to ya ambaci sunayen sojojin da suka ba shi wannan labari".

Magen ya maida martani "Na taba rubuta hakan, ina mamakin wace irin taba suke sha a fadar su, abun da Garba yayi ya kara tabbatar min da zargina.  

"Idan Garba ya yi tsammanin Ortom zai ba da bayanan mutanen da ke ba shi bayanai game da shirye-shiryensu, to lallai a fili ya wuce gona da iri.  

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci