OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar Jarabawa Ta NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawa Na 2022

Hukumar Jarabawa Ta NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawa Na 2

Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa wato NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta 2022.

Magatakardar hukumar Farfesa Dantani Wushishi ne ya bayyana sakamakon a ranar Alhamis a hedikwatar hukumar da ke Minna a jihar Neja.

Dantani ya bayyana adadin waɗanda suka yi rijistar jarabawar su 1,209,703 yayin da 1,198,412 suka zana jarrabawar.

Ya kuma bayyana cewa adadin waɗanda suka samu darasu biyar zuwa sama da suka hada da Ingilishi da Lissafi sun kai 727, 864 wanda ke wakiltar kashi 60.74 bisa dari.

Ɗantani Ya kuma ƙara da cewa adadin masu bukata ta musamman sun kai 1,031, da kuma kaso 98 sune zabiya, 574 masu nakasar ji, 107 kuma na fama da matsalar gani.

Baya ga haka, Wushishi ya ce an dakatar da masu kula da jarabawa 29, cewar Jaridar Punch.

Yayin da aka soke makarantu hudu na tsawon shekaru biyu saboda ayyukan da suka shafi badaƙalar jarabawa.

A cewarsa, raguwar satar jarabawa a lokacin jarrabawar ya yi kyau sosai in an kwatanta da baya.

"A fannin satar jarabawa ayyuka, an kama mutane 13,595 saɓanin 20,003 a shekarar 2021, wanda ya nuna raguwar yawan laifuka."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci