OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hatsarin Motoci a Kaduna ya yi sanadiyar rayuka 30 yayin da Motocin suka kone kurmus

Hatsarin Motoci a Kaduna ya yi sanadiyar rayuka 30 yayin da

Accident scene

Akalla mutane 30 ne aka ruwaito sun mutu sakamakon wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Zaria zuwa Kano a Jihar Kaduna.

Hatsarin wanda ya afku a ranar Alhamis da misalin karfe 5:30 na yamma ya janyo asarar ababen hawa wanda suka kone kurmus. 

A cewar wani ganau, hatsarin ya afku ne a kusa da Hawan Mai Mashi da ke karamar hukumar Makarfi a jihar.

Mataimakin kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Abdulrahman Yakasai ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yakasai ya ce hatsarin ya rutsa da motocin Toyota guda biyu masu kujeru 18 da wata motar Golf ta Volkswagen.

Yayin da yake mayar da martani kan musabbabin hatsarin, ya danganta lamarin da gudun wuce gona da iri. 

Ya kuma bayyana cewa an kwashe gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH), dakin ajiye gawa na Shika, Zariya yayin da wadanda suka samu raunuka ke samun kulawar likitoci a wannan asibitin.

Yakasai ya kara da cewa har yanzu ba a tantance lambobin motocin ba saboda konewar motocin kurmus. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci