OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hatsari Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 20 A Jihar Oyo

Hatsari Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 20 A Jihar Oyo

Sama da fasinjoji 20 ne aka ruwaito sun kone kurmus yayin da wasu biyu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a Lanlate, mahadar Maya a karamar hukumar Ibarapa ta Gabas a jihar Oyo.

Hadarin wanda ya hada da wata motar bas ta kasuwanci da wata mota kirar Sienna ya afku ne da yammacin ranar Juma'a.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne a sakamakon arangamar da ta yi sanadin barkewar gobara da ta cinye mutane sama da 20.

An kuma tattaro cewa fasinjoji biyu ne kawai suka tsira yayin da wasu kuma suka kone kurmus.

Shugaban karamar hukumar, Gbenga Obalowo wanda ya jagoranci tawagar masu Bada agajin gaggawa zuwa wurin ya bayyana abin a matsayin abin tausayi da takaici.

Don haka ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma bayyana cewa a halin yanzu mutanen biyu da suka tsira suna karbar kulawar a asibitin Awojobi da ke garin Eruwa, yayin da aka ajiye gawarwakin sauran fasinjojin a dakin ajiyar gawa.

Mista Gbenga Obalowa ya Kuma yi kira ga alumma dasu guji yin gudun wuce sa'a akan titunan domin zai iya haddasa asarar rayuka.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci