OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Taraba Ta Shirya Bada ‘Highland Tea’ Ga 'Yan Kasuwa

Gwamnatin Taraba Ta Shirya Bada ‘Highland Tea’ Ga 'Yan K

Governor Darius Ishaku of Taraba State

Gwamnatin jihar Taraba ta ce za ta mayar da dukkanin kamfanoninta hannun 'yan kasuwa domin gina wasu sabbi.

Manajan Daraktan Hukumar Zuba Jari da Rarraba Kadarori ta Jihar Taraba, Ezekiel Iliya ne ya bayyana hakan a Jalingo, babban birnin jihar.

Iliya ya ce ya zama wajibi hukumar zuba jarin ta gina kamfanonin gwamnati tare da mayar da su hannun 'yan kasuwa bayan an inganta su sosai.

Ya bayyana cewa, manufar da aka fi amfani da ita wajen dorewar kasuwancin jama’a ita ce mayar da kamfanoni hannun 'yan kasuwa. 

A cewar sa, nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta mayar da kamfanin Taraba Beverages Nigeria Limited masu sarrafa ganyen shayi na Highland Tea hannun 'yan kasuwa. 

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Iliya ya bayyana cewa: “Ba za mu sayar da kamfanin gaba daya ba, sai dai don mika tsarin mallakin gwamnati zuwa ga 'yan kasuwa.

“Muna sayar da kashi 75 cikin 100 na hannun jarin sa, kuma kashi 25 na gwamnati ne.

"Za mu tabbatar da cewa kwararrun mutane ne za su karbe kamfanin don tabbatar da dorewa."

Da yake yaba wa gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku bisa hazakar sa, ya kuma bayyana cewa a wani mataki na mayar da kamfanin Green House hannun 'yan kasuwa, gwamnati ta fara gyaran kamfanin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci