OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnan Katsina Ya Amince Da Janye Dokar Hana Hawa Babura

Gwamnan Katsina Ya Amince Da Janye Dokar Hana Hawa Babura

Gwamnan Jihar Katsina

Gwamnatin Katsina ta bayyana janye dokar haramta hawan babura daga bakin karfe goma na dare a duk fadin jihar.

Gwamnan Aminu Bello Masari ne ya bayyana janyewar ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Aminu Isa ya fitar a daren jiya Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa an janye dokar ne domin bawa al’umma damar gudanar da ayyukan ibada a watan Ramadana.

Wwatan Ramadana dai lokaci ne da al’ummar musulmi ke yawaita iada, wanda wasu ke tafiya tahajjud a masallatai daban-daban musamman a goman karshe.

Tun da fari dai gwamnatin Jihar Katsina ta sanya dokar hana hawa baburan ne daga bakin karfe goma na dare da a yunkurin dakile kai hare-hare da ‘yan bindiga ke yi.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci