OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

FRSC Ta Ce Ma'aikatan Ta Basu Fara Riƙe Makami Ba

 FRSC Ta Ce Ma'aikatan Ta Basu Fara Riƙe Makami Ba

Hukumar kare aukuwar haddura ta kasa ta bayyana cewa ma'aikatan ta basu fara amfani da makamai ba a yayin gudanar da Sintiri ko wasu aikace-aikace na hukuma. 

A wani jawabi ta bakin shugaban sashen wayar da kai na hukumar, Bisi Kazeem a birnin tarayya,  shugaban hukumar FRSC na wucin gadi, Dauda Biu, yace bayyana hakan ya zama dole sakamakon hotunan bidiyo na jami'in hukumar dauke da makami a bakin aiki daya karade shafukan watsa labarai. 

"Ina kira da al'umma da suyi watsi da sakon faifan bidiyo dake zagaye kafafen sada zumunta, saboda ma'aikacin hukumar kare aukuwar haddura ta kasa da aka gani dauke da makami na abokin sa ne a wata hukumar tsaro ya karaba don yin hoton bidiyo, kuma an dauke mataki da ya dace domin ladaftar da shi kan yin hakan. 

Biu, ya kuma ja hankalin al'umma da su guji yarda da labaran karya, ko wasu abubuwa makatmantan su domin bawa hukumar gudumawa wajen aiwatar da ayyukan ta na kare aukuwar hadura a titunan dake kasar nan.

 

NAN

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci