OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Darius Ishaku Ya Caccaki ‘Yan Majalisan Dake Cewa Ayyukan gwamnatin Tarayya Nasu Ne

Darius Ishaku Ya Caccaki ‘Yan Majalisan Dake Cewa Ayyukan

Governor Darius Ishaku of Taraba State

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya caccaki ‘yan majalisar dokoki daga jihar da suke yi ikirarin ayyukan gwamnatin tarayya a matsayin nasu.

Gwamnan wanda ya yi magana a yau (Litinin) yayin da yake ganawa da manema labarai a Jalingo ya ce abin bakin ciki ne ganin yadda ‘yan majalisa ke ikirarin ayyukan gwamnatin tarayya nasu ne maimakon su aiwatar da nasu.

A cewar sa, ya zama wajibi masu ruwa da tsaki su gargadi irin wadannan wakilai da ke ikirarin ayyukan da ba su aiwatar da su ba.

A cewar sa, gwamnatin jihar ta lura cewa wasu ayyuka na shiyya da kuma manyan ayyuka da 'yan Taraba suke kallo a matsayin aikin mutum daya maimakon ayyukan gwamnatin tarayya ba haka bane. 

Ya kuma koka da cewa: "Tsarin ganin ayyukan gwamnati a matsayin na mutum daya ya zama abin damuwa ga gwamnatin jihar."

Ya kara da cewa "Masu hakan su ne wakilan mu wadanda suka dauke dukiyar mu ta zama tasu."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci