OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dan majalisar tarayya ya jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa Borno

Dan majalisar tarayya ya jajantawa wadanda ambaliyar ruwa ta

Hon. Usman Zannah

Biyo bayan ambaliyar ruwa da ta afku a wasu sassan jihar Borno, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaga, Magumeri da Gubio, Usman Zannah ya ziyarci wadanda abin ya shafa a karamar hukumar Kaga ta jihar.

Zannah ya jajantawa wadanda abin ya shafa a yankunan Mainok, Benisheikh da Ngamdu dake karamar hukumar Kaga.

Da yake jawabi ga wadanda lamarin ya rutsa da su, ya ce ya yi matukar bakin cikin yadda ambaliyar ta haifar da asarar gonaki da gidaje.

Ya tausaya musu yana mai godiya ga Allah cewa ba a rasa rai ba.

Zannah wanda ya samu rakiyar dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar karamar hukumar Kaga, Mustapha Alibe Benishekh ya bukaci wadanda lamarin ya shafa da su dauki lamarin a matsayin jarrabawa daga Allah madaukakin sarki.

Dan majalisar ya kara tabbatar wa wadanda abin ya shafa cewa zai mika al’amuran su ga majalisar wakilai da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tallafa musu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci