OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Daliban Kwara Zasu Wakilci Najeriya A Gasar Muhawarar Makarantun Duniya

Daliban Kwara Zasu Wakilci Najeriya A Gasar Muhawarar Makara

Daliban makarantun sakandire a jihar Kwara na shirin wakiltar Najeriya a gasar muhawara ta makarantu ta duniya a kasar Netherlands a wannan shekarar.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kwara (KWSUBEB), Farfesa Sheu Raheem Adaramaja ya fitar.

Adaramaja ya bayyana cewa gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya kuma amince da shirin gudanar da atisayen wasa kwakwalwa ga daliban.

Ya ce atisayen na shirin shirya daliban ne domin fuskantar muhawarar gasar zakarun makarantun duniya.

Daliban da suka fito daga makarantun gwamnati a jihar sun lashe muhawarar makarantun kasa da aka yi a Legas don wakiltar Najeriya.

Adaramaja ya kara da cewa hakan ya bayyana cewa gwamnan ya zuba jari sosai a fannin ilimi.

A wani bangare sanarwar ta kara da cewa, “’ya’yanmu ne ke wakiltar Najeriya a kasar Netherlands.

"Mun haɗu da malamai daban-daban, ciki har da asalin masu harshen Ingilishi waɗanda ke da hannu a cikin shirin KwaraLEARN, don haɓaka ƙwarewar ɗaliban don su kasance mafi kyau."

Yayin da yake bayyana bukatar masu magana da harshen wajen shirya daliban, ya ce wani mataki ne na bayyana wa daliban harsuna daban-daban na turanci da za su iya haduwa da su a gasar.

Ya kara da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin ganin daliban sun zama zakara a duniya.

Ya ce, “Ana yin komai don ganin sun yi fice a gasar muhawarar makarantun duniya."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci