OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

CBN Basu Tuntube Ni Ba Game Da Chanja Fasalin Naira- Ministar Kudi

CBN Basu Tuntube Ni Ba Game Da Chanja Fasalin Naira- Minista

Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasar nan Zainab Ahmad ta gargadi Gwamnan bankin kasa CBN kan shirin da yake na sauya tsarin takardar kudi.

Zainab Ahmad na wanann batu ne lokacin da take kare kasafin kudin ma'aikatar ta na 2023.

Tace yin hakan zai zubar da darajar naira a kasashen duniya.

Tace ba ma a wannan lokacin ya dace a yi maganar sauya tsarin takardar kudin kasar nan ba.

Ministar Kudin ta kara da cewa, bankin kasar bai nemi shawarar ta ba, sai jin labarin shirin ta yi a kafafen yada labarai.

A ranar Larabar nan ne gwamnan bankin kasa Godwin Emefiele ya sanar da shirin sauya tsarin takardar kudi ta naira 200, naira 500 da kuma naira 1000 da nufin kawo cigaba a harkar kudin kasar nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci