OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Babbar Mota Ta Murƙushe Mace Mai Ciki Har Lahira A Ogun

Babbar Mota Ta Murƙushe Mace Mai Ciki Har Lahira A Ogun

Wani bala’i ya afku a ranar Juma’a yayin da wata babbar mota ta murkushe wata mata mai juna biyu da karamar yarinya a hanyar Abeokuta zuwa Ibadan a jihar Ogun.

Wakilin Jaridar Punch tattaro cewa motar da ke dauke da siminti ta kutsa cikin wani gini inda ta kashe mutane biyu tare da jikkata wasu hudu da ke cikin ginin.

Hadarin ya rutsa da wata Motar DAF mai lamba, BDJ 112 XF.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin a Abeokuta.

Akinbiyi ya bayyana cewa motar tana tafiya Ibadan daga Ewekoro lokacin da motar tafi ƙarfin direban ya rasa yadda zai yi ya kutsa cikin ginin.

Akinbiyi ya alakanta musabbabin hatsarin da yawan gudu da ya kai ga rasa iko wanda ya sa direban babbar motar ya ratsa ginin.

Ya ce an baza tawagar jami’an ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru domin hana matasan da suka fusata ɗaukan wani mataki.

Akinbiyi ya bayyana cewa an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na babban asibitin Odeda.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci