OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: Akwai yiwuwar kawo karshen yajin aikin da malaman jami'o'i ke yi-cewar Osodeke

ASUU: Akwai yiwuwar kawo karshen yajin aikin da malaman jami

 Shugaban kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Emmanuel Osodeke, ya ce nan ba da dadewa ba kungiyar za ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi.
Mista Osodeke ya bayyana haka ne a wani taro da sukayi da shugabannin majalisar wakilai a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce daga yanda taron ya gudana “kungiyar ta hango haske a lamarin.

" wannan karon muna sa rai cewa ba za a samu wasu mutane ko kungiya da za su haifar da abinda zai hana kungiyar janye yajin aiki.

Ya kuma yi fatan cewa shiga tsakani da shugabannin majalisar su ka yi zai kawo karshen yajin aiki saboda dalibai, inda ya kara da cewa fafutukar da ASUU ta yi ne saboda ilimi da jami’o’i a kasar nan.

“Muna fatan nan da ‘yan kwanaki masu zuwa za mu kawo karshen wannan yajin aikin.

Muna son a samar da tsarin da zai iya jawo malamai a fadin duniya zuwa jami’o’inmu,” in ji Mista Osodeke.

Ya ce ya kamata kuma a rika biyan jami’o’in Najeriya da kudi mai tsoka domin jawo hankalin daliban kasashen waje, yayin da ya nuna damuwa kan wasu nagartattun malamai da ke barin kasar.

Ya ce yajin aikin bai kamata ya wuce makonni biyu ba, “inda majalisar dokokin kasar ta sa baki tun da jimawa ”.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci