OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Jami'ar Babcock tace zatayi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da an gurfanar da wadanda suka kashe farfesa Olowojobi

Jami'ar Babcock tace zatayi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da

Babcock Teaching Hospital, Ilisan-Remo

Hukumar gudanarwar Jami’ar Babcock dake jihar Ogun, a ranar Talata, ta bayyana cewa jami’an tsaro na gudanar da bincike kan kisan Farfesa Yinka Olomojobi, tare da bayar da tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu.

 

An harbe farfesa Olomojobi, dake koyarwa a fannin kare hakkin dan adam a jami’ar a daren ranar Juma’ar da ta gabata, da misalin karfe 9 na dare.

Rahotanni sun tabbatar da ‘Yan bindigar sun kai kimanin takwas, sanye da bakaken kaya, sun harbe Olomojobi bayan yayi gardama a lokacin da sukayi kokarin yin garkuwa da shi kamar yadda wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Omolola Odutola ta fitar.

 

SP Odutola ta ce tuni ‘yan sanda suka kama wani Awada Ishaya daga jihar Filato da suke zargin yana da hannun a kisan malamin.

 

Sai dai daraktan sadarwa na jami'ar Dokta Joshua Suleiman, yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya, ya ce tuni jami’an tsaro na kan bin diddigin wadanda suka kashe malamin nasu.

 

Suleiman ya ce “Jami’ar ta sanar da iyalan marigayin a hukumance faruwar lamarin. Jami’an tsaron dake aiki a jami'ar suma suna taimakawa yan sanda wajen binciken saboda haka muna da tabbacin nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda suka yi kisan. 

 

“Game da tsarin jana’izar, wannan ya rage ga iyalansa su yanke shawara amma jami’ar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin abin da ake bukata a irin wannan yanayi. Muna tabbatar wa dalibanmu da iyayen su da ma’aikatanmu da malamai da masu fatan alheri cewa jami’ar Babcock wuri ne mai aminci da inganci don yin karatu da aiki kuma munyi alkawarin sauke nauyin da aka dora mana”.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci