OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ƴan Ta'adda Sun Kashe Mutane 11 a Masallacin Juma'a a Zamfara

Ƴan Ta'adda Sun Kashe Mutane 11 a Masallacin Juma'a a Zamfa

Wasu ƴan ta’adda da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kashe mutane 11 a cikin masallaci a jihar Zamfara.

Rahoton Daily Nigerian yace waɗanda suka mutu sun haɗa da ƴan kauyen Ruwan Jema ne a jihar.

Yayin da rahoton ya ce cewa wasu gungun ƴan ta’adda ne a cikin ayarin babura suka kai farmaki garin Ruwan Jema yayin da masallata ke salla ranar Juma’a.

Ɗaya daga cikin majiyoyin, Aliyu Nnarki, wanda ya kasance mazaunin garin Ruwan Jema ne, yace ƴan bindigar sun far wa al’ummarsu ne a lokacin Sallar Juma’a a cikin masallacin.

"Waɗanda ƴan fashin suka kashe na daga cikin waɗanda suka yi sallar Juma'a a masallaci".

Bayan samamen da ƴan ta’addan suka kai, duk da cewa mutane da dama sun bace tun jiya, amma an gano gawarwaki 11 na mutanen wannan yankin.

Jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma sun daɗe suna fama da hare-haren ƴan bindiga.

Yayin da a kullum gwamnatin tarayya ke alƙawarin kawo ƙarshen rashin tsaro a nan da watan Disamba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci