OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

An Maka Ɗalibi A Kotu Bisa Zargin Satar Waya

An Maka Ɗalibi A Kotu Bisa Zargin Satar Waya

An maka wani dalibi mai suna Michael Okolie ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Ogudu a jihar Legas bisa zargin satar waya.

Ɗalibin wanda bai wuce shekaru 27 ba, ana tuhumansa da abu biyu da suka haɗa da haɗa baki wajen yin sata.

Sufeto Sunday Bassey, mai gabatar da ƙara, ya shaida wa kotun cewa wanda ake ƙara da wasu mutane sun haɗa baki wajen sace wayar da ta kai Naira 56,000.  

Mutanen sun yi satar ne a ranar 3 ga Oktoba da karfe 11:30 na safe a filin lambun Abiola, a titin Ojota Expressway, jihar Legas, 

A cewar Bassey, Okolie ya rage wa wanda ya ɗauke shi a  matsayin fasinja a motarsa inda suka ƙulla makirci da wasu don sace wayar yayin da yake sauka daga motar.

Mai gabatar da ƙara ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 411 da na 287 na dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin a gaban Alkalin Kotun Mai shari’a O.A.  Dauda.

Yayin da Mista Daudu ya bayar da belin Okolie a kan kudi Naira 50,000 tare da mutum biyu masu tsaya masa, inda ya ba da umarnin a tabbatar da adireshin gida da ofis na waɗanda za su tsaya.

Alƙalin kotun ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba domin sauraren ƙarar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci