OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ambaliyar Ruwa Ya Kashe Ƙaramin Yaro Da Wasu Mutum Biyar a Kogi

Ambaliyar Ruwa Ya Kashe Ƙaramin Yaro Da Wasu Mutum Biyar a

Photo Source: The Eagle Online

Aƙalla mutane shida ne, ciki har da wani ƙaramin yaro, aka sanar sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye daukacin karamar hukumar Ibaji ta jihar Kogi.

Biyu daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su an same su ne a bakin teku biyo bayan wani kwale-kwale da ya kife a ranar Talata.

Abun ya faru ne a lokacin da kwale kwalen ke ƙoƙarin tsallakar da mazauna ƙauyen Ganaja daga yankin Gadumo a Lokoja.

Rundunar ƴan sandan jihar Kogi ta tabbatar da hakan a ranar Laraba ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP William Aya, cewar Jaridar Punch.

"Eh, zan iya tabbatar da cewa an gano gawarwakin mutane biyu biyo bayan wani hatsarin kwale-kwale a ranar Talata a lokacin da suke kokarin jigilar mazauna yankunan da ambaliyar ruwa ta mamaye titin Ganaja-Lokoja."

Har ila yau, shugaban ƙaramar hukumar Ibaji, Williams Iko-Ojo, yayin da yake zantawa da manema labarai ya ce  mutane hudu sun mutu ciki har da wani ƙaramin yaro baya ga lalata daukacin gonakin karamar hukumar.

“Kamar yadda nake magana da ku a halin yanzu, babu wata ƙasa guda ɗaya da za a iya rayuwa a Ibaji, ko’ina ya nutse kuma mutane na cikin wani yanayi mai muni.

“A gaskiya matsalar jin kai ta fi karfin abin da kananan hukumomi za su iya magancewa kuma muna kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da dukkan hukumomin da abin ya shafa da su kawo agaji.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci