OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Abin Da Buhari Yace Game Da Sake Nnamdi Kanu

Abin Da Buhari Yace Game Da Sake Nnamdi Kanu

Hoto Daga: Vanguard

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai saki shugaban haramtacciyar Kungiyar 'yan awaren nan na Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu ba.

Ya ce kamata ya yi shugaban ‘yan awaren ya kare kansa a gaban kotu bisa zargin sa na bayanan karya game da gwamnatin Najeriya a lokacin da yake kasar waje.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a daren Laraba.

A shekarar da ta gabata ne Buhari ya shaida wa wasu dattawan kudancin kasar cewa ba zai so ya tsoma baki a harkokin shari’a ba amma ya ce zai duba bukatar su akan sakin Kanu duk da ganin hakan na da wahala.

A cewar shugaba Buharin, “Akwai wata cibiya da ba zan tsoma baki a kai ba, wato bangaren shari’a. Lamarin Kanu na bangaren shari’a ne amma abin da nake mamaki shi ne lokacin da Kanu ya yi zaman sa cikin lafia a Turai yana cin zarafin wannan gwamnatin tare da ambaton abubuwa da dama, ina tsammanin yana so ya zo ya kare kansa ne akan zargin.

“Don haka muna ba shi damar kare kansa a tsarin mu, ba wai ya rika cin zarafi daga Turai kamar ba dan Najeriya ba. Bari ya zo nan tare da mu sannan ya kushe mu a nan. ’Yan Najeriya sun san ba na tsoma baki a harkokin shari’a, a saurare shi. Amma masu cewa a sake shi, a’a, ba za mu iya sake shi ba.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci