OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Kwankwaso Yayi Kira Da a Hada Kai Don Cinma Manufa

2023: Kwankwaso Yayi Kira Da a Hada Kai Don Cinma Manufa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kira ga hadin kan ‘yan Najeriya yayin da magoya bayan sa suka tarbe shi a Jihar Kogi.

Kwankwaso yayi kiran ne a ranar laraban da ta gabata. 

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kwankwaso ya yi wannan kiran ne a Lokoja, yayin da yake kaddamar da ofishin yakin neman zaben sa da kuma sakatariyar jam’iyyar a Kogi.

Jim kadan bayan isowar sa ofishin yakin neman zaben dake makwabtaka da Dave Mercy Pharmacy, dake kan titin gidan gwamnatin Kogi, magoya bayan sa sun yi masa tarba mai kyau, inda suka rera wakokin yabo da rawe-rawe. 

Da yake jawabi ga dimbin jama’ar kasar, Kwankwaso ya bayyana cewa Najeriya na matukar bukatar shugaba mai hangen nesa kuma amintacce wanda zai iya kawo ci gaban da ake bukata.

“Bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba, sai dai mu tashi tsaye wajen ganin mun ceto kasar nan daga dukkan kalubalen da take fuskanta ta hanyar amfani da katin zaben mu na din-din-din (PVC).

“Zaben da ke tafe a shekarar 2023 wata babbar dama ce ga dukkan ‘yan Najeriya wajen hada kan dan takarar shugaban kasa nagari wanda zai iya kawo sauyi,” inji shi.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, bayan nasarar kaddamar da ofishin yakin neman zaben da sakatariyar jam’iyyar, ya ziyarci gidan tsohon gwamnan jihar, Marigayi Prince Abubakar Audu.

Da yake jawabi a ziyarar, daya daga cikin masu taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yada labarai, Musa Yunusa, ya bayyana jin dadin sa da tarbar da aka yi wa dan takarar.

Yunusa, ya bayyana Kogi a matsayin gidan Kwankwaso kuma liyafar da aka yi masa alama ce ta karbuwar sa a matsayin wanda zai iya jagorantar al’ummar kasar zuwa ga wani matsayi mai girma idan aka samu dama a 2023.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci