OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zulum yayi jawabi ga kungiyoyin kasa-da-kasa akan Ilimin yara mata a New York

Zulum yayi jawabi ga kungiyoyin kasa-da-kasa akan Ilimin yar

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi jawabi ga kungiyoyin kasa da kasa kan ilimin yara mata a birnin New York na kasar Amurka.

Jawabin gwamnan don a kara mayar da hankali kan ilimin ‘ya’ya mata a Najeriya da ma duniya baki daya ne. 

Gwamnan yaje Amurka ne a cikin tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 (UNGA77) da aka gudanar a hedikwatar majalisar dake birnin New York.

An gayyaci Zulum ne a matsayin babban bako mai jawabi a wani shiri mai taken ‘Rewrite the Future’ wanda aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata, domin jawo hankalin masu zuba jari a fannin ilimin ‘ya’ya mata a duniya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau ya fitar yau (Asabar) ya ce “Zulum ya gabatar da jawabi mai taken zuba jari a ilimin ‘yan mata a Najeriya, inda ya mayar da hankali kan jihar Borno.

A cewar sanarwar, Zulum ya bayyana cewa, a wani kokari na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi a Najeriya, an kaddamar da shirye-shirye na tallafa wa ilimin yara mata.

Ya bayyana shirye-shiryen kamar na BESDA da kuma shirin AGILE. 

“A yankin arewacin jihar Borno, gibin ilimin yara mata ya yi yawa.

"Muna bukatar karin malamai, karin horar da malamai, kayan aikin dakin gwaje-gwaje da dai sauran su domin baiwa yaran mu damar samun ingantaccen ilimi," in ji Zulum.

Gwamnan ya ce tsarin ilimi na jihar ya kara tabarbarewa sama da shekaru 12 na rikicin Boko Haram wanda a yanzu ya ragu.

Ya ce baya ga mutuwar sama da mutane 100,000 da kuma raba kimanin miliyan biyu da muhallan su, maharan sun kai hari makarantu da dama.

A cewarsa: "Sama da gine-ginen makarantu 5,000 ne Boko Haram suka lalata."

“Sama da malamai 530 ne aka kashe, an sace dalibai da dama, kuma an sace su aka tura su Boko Haram a matsayin ‘yan leƙen asiri ko yara mayaka, yayin da aka kashe wasu."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci