OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

‘Yan Sanda A Katsina Sun Ceto Ɗan Takarar Majalisa Daga  Hannun ‘Ƴan Ta’adda

‘Yan Sanda A Katsina Sun Ceto Ɗan Takarar Majalisa Daga 

Photo Source: Legit Hausa

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, a daren ranar Asabar, sun ceto dan takarar majalisar dokokin jihar mai wakiltar Kankia na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Ibrahim Tafashiya, daga hannun ‘yan ta’adda.

A daren jiya ne ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da Tafashiya a karamar hukumar Kankia da ke jihar.

An sanar da ’yan sanda game da garkuwa da shi, lamarin da ya sa jami’in ‘yan sanda reshen Kankia, Sufeto Ilyasu Ibrahim da tawagarsa suka tare hanyar fitarsu tare da yin artabu dasu inda aka ceto Tafashiya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.

Isah ya kara da cewa "Gaskiya ne tawagarmu ta kubutar da Tafashiya daga hannun 'yan ta'adda harma ya sake haduwa da iyalansa."

An kuma bayyana cewa, wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki gidan magatakardar Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita Salisu Gide da ke Kankia, inda suka yi awon gaba da shi da matarsa.

Jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar kubutar da Gide a wannan dare, yayin da ake ci gaba da kokarin kubutar da matarsa ​​da sauran wadanda ‘yan ta’addan suka sace har zuwa safiyar Lahadi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa an ga ‘yan ta’addan a wani wuri da ke kusa da karamar hukumar Batsari.

A halin da ake ciki kuma, wasu ‘yan ta’adda sun kai hari da sanyin safiyar Lahadi a Sabuwar Kwata da ke karamar hukumar Jibiya ta jihar inda suka yi awon gaba da wani mutum da yara biyu.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da sassafen ranar Lahadi. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci