OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan garin Chibok sun koka kan halin ko in kula kan 'yan mata 110 dake hannun Boko Haram

'Yan garin Chibok sun koka kan halin ko in kula kan 'yan mat

Chibok girls| Photo Source: Aljazeera

Kungiyar Cigaban yankin Kibaku (KADA) a jihar Borno ta koka kan yadda aka yi watsi da wasu ‘yan mata sama da 100 da kungiyar Boko Haram ta sace a shekarar 2014.

An sace ‘yan matan da yawan su ya kai 276 daga makarantar sakandaren mata a karamar hukumar Chibok da ke jihar.

Tun bayan sace su, 57 daga cikin su sun tsere da kan su yayin da 110 suka rage a hannun 'yan ta'addan. 

Kungiyar wadda ta bayyana hakan a yau (Laraba) ta ce gwamnati ta nuna karfin ta bayan an sako sauran wadanda harin jirgin kasa ya rutsa da su daga Abuja zuwa Kaduna.

Kungiyar ta yi zargin cewa da faruwar hakan, suna da hujjar cewa gwamnati ta yi watsi da lamarin ‘yan matan na Chibok. 

A cewar shugaban kungiyar na kasa, Dauda Iliya: “Batun watsi da ‘yan matan makarantar Chibok ya sake fitowa bayan sako sauran wadanda aka sace daga jirgin kasa da aka yi garkuwa da su, musamman saboda kokarin gwamnatin tarayya da ma sojoji a karkashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro, Lucky Irabor.

"Maganar musamman ta jawo wa 'yan Chibok raɗaɗi a zuciya tare da tunanin rashin kulawa da watsi daga gwamnatin tarayya."

Ya kuma koka da yadda al’ummar ke fuskantar hare-hare iri-iri duk da cewa ‘yan matan na hannun 'yan ta'addan haryanzu.

A cewar Punch, Iliya ya ce: "Harin na baya-bayan nan a Chibok ya faru ne a ranar 3 ga watan Oktoba na 2022, a Njlang, wani kauye mai nisan kilomita 5 daga Chibok."

Ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum da su kara kaimi wajen ganin an ceto su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci