OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Bindiga Sun harbe Yansanda Biyar Da Fararen Hula Uku har lahira A Katsina

Yan Bindiga Sun harbe Yansanda Biyar Da Fararen Hula Uku har

Akalla ‘yan sanda biyar da fararen hula uku ne aka kashe a wani harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Gatikawa da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

Rahotanni sun ce an kai harin ne da yammacin ranar Laraba.

‘Yan sandan sun je aiki na musamman ne daga Kano lokacin da ‘yan fashin suka kutsa garin. 

Sautin makamansu ya firgita jama'a yayin da suke harbe-harbe a kan babura a cikin garin. 

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun haura 300 a lokacin da suka mamaye garin..

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan fashin sun rika bi gida-gida suna neman kudi, kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.

Majiyar ta bayyana cewa mutane da dama sun jikkata yayin da suke kokarin tsere wa harin.

Harin ya tilasta wa wasu mazauna yankin fakewa a wasu garuruwa da ke makwabtaka da su saboda fargabar sake kai hari.

Idan dai ba a manta ba ‘yan bindiga sun kashe wani babban dan sanda a karamar hukumar Dutsinma da kuma mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Aminu Umar tare da wasu fararen hula.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya aika wa Jaridar Daily Trust. 

Ya ce, “Gaskiya an kashe ‘yan sanda biyar daga Kano da ke aiki na musamman a Kankara da mutanen kauyen Gatakawa uku."

A wani labarin kuma, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda ya ce rundunar ‘yan sandan ta dukufa wajen ganin ta kyautata rayuwar mutanenta tare da gabatar da cak na N14.6m ga iyalai da ‘yan uwan ​​‘yan sandan da aka kashe a bakin aiki.

Ya ce yana gabatar da cak din ne a madadin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta kara da cewa, matakin na daga cikin shirin Inshorar jin dadin iyali na IGP na musamman domin kula da iyalan jami’an da suka mutu a bakin aiki.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci