OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yadda Yara 42 da Mata Masu Juna Biyu Suka Kubuta Daga Hannun Turji a Zamfara

Yadda Yara 42 da Mata Masu Juna Biyu Suka Kubuta Daga Hannun

Rundunar 'yansandan jihar Zamfara sun tabbatar da tsiran mutane 97 daga hannun hatsabibin dan ta'addan nan, Bello Turji.

Anyi karguwa da mutanen ne a kananan hukumomin Shinkafi da Tsafe na Jihar Zamfara.

Bayanin tsiran mutanen yazo ne cikin hira da manema Labarai da kwamishinan 'yansandan jihar, Ayuba Elkanah ya gudanar ranar talata.

Yayin da yake bayanin, yace mata masu juna biyu bakwai, jarirai goma sha tara, da kuma kananan yara goma sha shida ne suka kubuta.

A cewar kwamishinan, sakamokon matsin lamba da jami'an tsaro suka kai sansanin kasurgumin dan ta'addan nan, Bello Turji, rundunar 'yansandan sun samu rahoton sirri cewa an ga wasu da akayi garkuwa da su a makale cikin dajin.

Ya kara da cewa an ceto mutanen ne cikin hadin gwiwa da ‘yan ta’addan da suka tuba tare da ‘yan banga.

Mutanen da aka ceto sun kai kimanin watanni uku a hannun Turji.

Elkanah ya ce dukkan wadanda aka ceto din sun samu kulawar likitocin gwamnatin jihar da na ‘yan sanda.

Ya bayyana cewa za a mika su ga gwamnatin jihar kafin a sake hada su da iyalan su.

Kwamishinan yayi godiya da jinjina wa gomnan jihar Zamfara, Bello Matawalle bisa goyon baya da jagorancin sa na ganin cewa an kawo karshen aiyukan ta'addanci a jihar.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci