OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Sojoji Sun Dakile Yunkurin Sace Wani Malamin Katolika a Imo

Sojoji Sun Dakile Yunkurin Sace Wani Malamin Katolika a Imo

Rundunar sojin Najeriya tayi nasarar dakile yunkurin sace wani malamin Katolika na Orlu Diocese, Reverend Augustine Ukwuoma.

Lamarin ya faru ne a Sakatariyar Katolika ta Orlu, dake kan titin BSC a jihar Imo.

A ranar Lahadi ne da misalin karfe 2:30 na safe sojojin suka amsa kiran gaggawa inda suka ceto malamin.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, Daraktan hulda da jama’a na rundunar, sojoji za su ci gaba da dakile aiyukan masu aikata laifuka.

Dakarun da ke gudanar da atisayen ‘Golden Dawn Sector 3’ ne Suka dakile yunkurin yin garkuwa da Reverend Augustine. 

Nwachuckwu ya kara da cewa, sojoji sun yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru inda suka dakile harin kana maharan suka gudu.

“Sojoji za su ci gaba da daina ba da ‘yancin tada tarzoma ga 'yan haramtacciyar kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra / Eastern Security Network (IPOB/ ESN) da sauran gungun masu aikata laifuka da ke aiki a bangaren musamman a daidai lokacin da zaben jihar Anambra ke kara gabatowa da kuma bukukuwan karshen shekara," kamar yadda sanarwar ta kunsa.

 

Rundunar ta kuma shawarce Jama'a da su kai rahoton duk wani yunkuri na masu aikata laifuka da kuma maboyar haramtacciyar kungiyar IPOB/ESN ga hukumomin tsaro.

 

Ya kara da cewa kungiyar bata da aiki illa tsoratarwa da cin zarafin mutane, yin garkuwa da mutane don karban kudin fansa. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci