OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sanatan PDP Ya Mallaki Ofishin Yakin Neman Zaben Buhari a Daura

Sanatan PDP Ya  Mallaki Ofishin Yakin Neman Zaben Buhari a D

Ekiti 2022-PDP

Sanata mai wakiltar Katsina ta Arewa shiyyar Daura, Ahmad Babba Kaita, ya karbe ofishin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura.

Premium Times ta tattaro cewa ofishin yakin neman zaben da ke tsakiyar garin Daura, mahaifar shugaba Buhari, a baya ofishin ya kasance mallakin kungiyar The Buhari Organisation (TBO) wanda ta kafa ta a shekarar 2002 lokacin da ya shiga jam’iyyar All People’s Party a karon farko a shekarar 2003.

Kaita wanda ya tsallaka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a watan Afrilun wannan shekarar.

Ya zargi gwamnan jihar, da rashin tsoma masu ruwa da tsaki a harkar gwamnatin sa da kuma rashin gudanar da zaben kananan hukumomi, rashin biyayya ga kafuwar dimokuradiyya da rashin samar da daidaito ga masu ruwa da tsaki a jihar.

Ofishin, wannda aka tattaro cewa, a da mallakin yan jam'iyyar shugaban kasa Buhari ne amma a makon da ya gabata Sanatan ya sayi ofishin daga hannun su.

Har ila yau ofishin ya tara ‘ya’yan jam’iyyar APC da dama da suka hada da jiga-jigan zartaswar jam’iyyar a Daura.

Bayan ya siya, Sanatan ya mikawa jam’iyyar PDP domin ta zama babban ofishin jam'iyyar na karamar hukumar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci