OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rundunar Soji: Dalilin da ya sa ba za mu bi umarnin kotu mu maido da jami'in mu aiki ba

Rundunar Soji: Dalilin da ya sa ba za mu bi umarnin kotu mu

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta mutunta umarnin da kotu ta bayar na mayar da Kanal Danladi Hassan da aka kora daga aiki a shekarar 2016 ba.

 

A cikin wata wasika da rundunar ta aike wa kwamitin majalisar wakilai kan kararraki mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Oktoba, rundunar ta kuma ce ba za ta biya jami'in kudadensa na sharia da albashi da kuma alawus-alawus ba kamar yadda kotu ta umarta.

 

Mista Hassan, wanda shi ne ya jagoranci sojoji suka kwato garin Bulabulin da Damboa daga hannun 'yan Boko Haram a shekarar 2014, an yi masa ritayar dole ne a shekarar 2016.

 

An yi masa ritaya tare da wasu jamiai 37 ba tare da kwakkwaran dalili ba.

 

Bayan ya yi ritayar dole, sai ya shigar da kara a kotun masanaantu ta kasa (NIC) wacce a watan Janairun 2019 ta ba da umarnin a dawo da shi bakin aiki.

 

Alkalin kotun, Sanusi Kado, ya ce rundunar soji ta kasa shawo kan kotu kan cewa kokarin ladabtar da shine ya sa aka yi masa ritayar dole.

 

Hukuncin da NIC ta yanke shi ya tilastawa rundunar sojin daukaka kara kan hukuncin da aka yanke.

 

Rashin bin umarnin kotun ne ya sa jamiin ya roki majalisar wakilai da ta tilasta wa rundunar sojin ta mayar da shi bakin aiki tare da biyansa hakkinsa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci