OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rashin tsaro: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyen Benue, Sun Kashe Mutum Uku

Rashin tsaro: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyen Benue, Sun Kas

A wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Ngban da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue, an kashe mutane uku.

Lamarin da ya sa mutanen kauyen suka kaurace wa gidajen su ya faru ne a daren Lahadi.

Wani mazaunin garin mai suna Abel a wata hira da Daily Trust ya ce ‘yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 7 na dare.

A cewar sa: “An kashe wata mata a nan take yayin da sauran biyun suka mutu jim kadan bayan harin sakamakon raunukan da maharan suka yi musu.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene ita ma ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce an kashe mutane uku a harin da aka kai daren Lahadi.

Ta kuma bayyana cewa an kai gawarwakin mamatan zuwa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue (BSUTH).

A cewar ta: “An kashe mutane uku a wani hari da aka kai a Guma, an kwashe gawarwakin zuwa BSUTH yayin da ake ci gaba da bincike”.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan bindigan suka tare hanyar Daudu zuwa Lafiya kusa da gonar NYSC da ke Uda Yagba inda suka yi wa masu wucewa rauni.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci