OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rashin Tsaro: An Kama Masu Garkuwa Da Mutane 540 A Cikin Wata Guda – FG

Rashin Tsaro: An Kama Masu Garkuwa Da Mutane 540 A Cikin Wat

A yau Litinin gwamnatin tarayya ta bayyana cewa rundunar sojin Kasarnan da ke aiki tare da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a cikin watannin Yuli da Agusta, sun kama jimillar mutane 540 da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da kubutar da wasu mutane 299 da aka yi garkuwa da su a kokarin magance kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

An kuma kama jimillar mutane 778 da ake zargi da yin fashi da makami yayin da aka kama mutum 3,394 bisa wasu laifuka daban-daban. Haka zalika anyi nasarar kwato makamai 458 da harsashi 4,658 a hannun bata garin. 

Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi me ritaya ne ya bayyana haka a wajen wani taron na musamman kan nasarorin da ake samu wajen dakile matsalar rashin tsaro a kasar nan.

Sakamakon Rahoton ya nuna cewar, a shiyyar Arewa ta tsakiya, an kama mutane 100 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, 84 da ake zargi da aikata fashi da makami, yayin da aka ceto mutum 12 da aka yi garkuwa da su.

A yankin Arewa maso Gabas, an kama mutane 174 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, Mutum 107 kuma an kama su da laifin fashi da makami, an kuma ceto mutane 32 da aka yi garkuwa da su.

 A yankin Arewa maso Yamma, an kama mutane 136 da ake zargi da yin garkuwa mutane, an kama 128 da laifin fashi da makami, sannan an ceto mutane 62 da aka yi garkuwa da su.

A yankin Kudu maso Gabas, an kama mutane 39 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, 36 kuma an kama su da laifin fashi da makami, yayin da aka ceto mutum 24 da aka yi garkuwa da su.

A yankin Kudu-maso-Kudu, an kama mutane 30 da ake zargi da yin garkuwa, an kuma kama mutane 58 da ake zargi da aikata fashi da makami, sannan an ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su.

A yankin Kudu maso Yamma, an kama mutane 61 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, 174 da ake zargi da aikata fashi da makami yayin da aka ceto mutane 5.

Ministan ya kara da bayyana cewa an samu zaman lafiya a da yawa daga cikin manyan hanyoyin kasar da a baya suke fuskantar harin bata gari kamar Abuja-Kaduna, Kaduna-Birnin – Gwari, Sokoto-Zamfara, da Zamfara-Kaduna.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci