OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

NEMA Ta Rarraba Kayayyakin Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Ritsa Dasu A Katsina

NEMA Ta Rarraba Kayayyakin Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa T

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta raba kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomi 13 na jihar Katsina a kokarin gwamnatin tarayya na rage radadin wadanda bala’in ya shafa a kasar nan.

Ministar Jin kai da bada agaji Sadiya Umar Farouq ce ta mika kayayyakin ga Gwamnatin Jihar Katsina a yammacin Alhamis a dakin ajiyar kayayyakin agaji na Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Katsina.

Ta ce kayayyakin agajin sun hada da buhunan shinkafa, masara da wake 9,000, buhunan siminti 1,000, buhunan rufin kwano 300, man girki garwa 20, Sinadarin dandano 200, gishiri 300, fakiti 100 na kusoshi.

Sai Kuma  katifu 500, barguna 1,000, tabarmi 5,000, gidajen sauro guda 2,000, Atamfofi guda 500 da kuma tufafin yara guda 1,000.

A jawabin ta yayin taron Sadiya Umarfaruk ta ce sun kawo kayan ne musamman domin wadanda iftila'in ambaliya ya abkawa a Kananan hukumomi 13. Ta Kuma bukaci mahukuntan su tabbatar Kayayyakin sun isa hannun waɗanda abin ya shafa.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Tasiu Musa Maigari wanda ya karbi kayayyakin a madadin gwamnati, ya bada tabbacin cewa za a raba kayayyakin ne ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da ta samar da kayayyakin agaji ga wadanda abin ya shafa, ya kuma kara da cewa wannan tallafin zai taimaka matuka wajen rage musu radadin da ambaliyar ruwa ta haddasa a yankunansu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci