OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane 9 Sun Mutu Yayin Da 10 Suka Jikkata A Wani Hatsarin Mota A Abuja

Mutane 9 Sun Mutu Yayin Da 10 Suka Jikkata A Wani Hatsarin M

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane 9 tare da jikkatan wasu goma a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Yangoji zuwa Abaji, dake babban birnin tarayya Abuja.

Kakakin hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa FRSC Bisi Kazeem ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Mista Kazeem ya ce hatsarin ya haɗa da wata mota kirar Toyota Hiace Bas mai lamba KTG-450 KQ da kuma motar Howo Sino a kan hanyar Yangoji zuwa Abaji da misalin karfe 6:05 na safiyar Lahadi.

Ya ce motar bas din ta taho ne daga Osun yayin da ta nufi jihar Katsina, amma abin takaici ta fada kan wata tirela da ke tsaye.

“Mutane 22 ne suka shiga hatsarin, Dukkansu maza ne, goma sun jikkata sannan tara sun mutu.

"An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibiti, Abaji a motar ‘yan sanda da ke sintiri.

“An ajiye gawarwakin mutane tara a dakin ajiye gawa a babban asibitin Kwali, Abuja sannan kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya, sashin Kwali ya dauki nauyin gudanar da bincike,” inji shi.

Mista Kazeem ya ruwaito Mukaddashin Rundunar FRSC, Dauda Biu, yana cewa haɗarin ya samo asali ne daga ratse mai hatsarin gaske, wanda direban ya gagara shawo kan motar.

Mukaddashin rundunar Marshal ya jaddada cewa haɗarurruka da daddare sun fi yin muni fiye da lokacin rana.

Ya nanata cewa, hukumar za ta rubanya kokarin ta ta hanyar wayar da jama’a masu ababen hawa a duk fadin kasar nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci