OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Makiyaya Dauke Da Makamai Sun Kutsa Kauyuka 4 a Jihar Benue

Makiyaya Dauke Da Makamai Sun Kutsa Kauyuka 4 a Jihar Benue

Hoto Daga: PremiumTimes

An samu tashin hankali a wasu kauyuka 4 na karamar hukumar Logo ta jihar Benue yayin da wasu makiyaya dauke da makamai suka kutsa, lamarin da ya sa mutane cin na kare.

 

Yankunan da abin ya shafa sun hada da kauyukan Turan, Yonov, Tombo da Nenzev.

 

Rahotanni sun ce makiyayan sun mamaye kauyukan da dama kuma suna cin karen su ba babbaka.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani mai magana aji a yankin, Joseph Anawah ya bayyana cewa makiyayan dauke da makamai sun zo da shanunsu dubbai a ranar Talata.

 

Yayin da ba a fitar da wata sanarwa a hukumance daga rundunar ‘yan sanda a jihar ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, sakataren kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), reshen jihar Benue, Ibrahim Galma ya ce ba ya gari, amma zai yi magana muddin ya samu cikakkun bayanai.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci