OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Direba Tare Da Awun Gaba Da Fasinjoji

Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Direba Tare Da Awun Gab

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani direba tare da yin garkuwa da wasu fasinjoji da ba a tantance adadin su ba a hanyar Funtua zuwa Dandume a jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne da karfe 7:45 na yammacin ranar Lahadi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Isah ya ce an harbe mutane uku a yayin harin.

Ya bayyana cewa: “Daya daga cikin direbobin ya mutu, sauran biyun da aka harbe an kai su asibiti. Har yanzu ba a samu wani labarin fasinja da aka sace ba."

Da yake zantawa da Daily Trust a wata hira, wani direba mai suna Bello Halilu ya bayyana cewa: “Wannan lamari ya faru ne a Kwanar Gamji da ke kusa da Hawan-Fulani.

“’Yan bindigan sun yi kwanton bauna ne inda suka bude wuta kan motocin da ke tafiya, inda suka kashe direba daya tare da yin awon gaba da fasinjoji da ba a tantance adadin su ba.

"Wasu da suka tsere sun kwana a cikin gonaki."

Ya kuma bayyana cewa hanyar ta kasance babu kowa a kodayaushe saboda ayyukan ‘yan bindiga sai dai a ranakun kasuwa.

A cewar sa: “Kamar jiya (Lahadi), wasu direbobi sun yi kokarin bin hanyar domin harkokin tattalin arzikin da ke bunkasa a wannan lokacin na girbi.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci