OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kada Ku Yi Maƙarƙashiya Da 'Yan Siyasa - NUJ

 Kada Ku Yi Maƙarƙashiya Da 'Yan Siyasa - NUJ

Meet Sam Udekwe The New NUJ Chairman, Enugu State Chapter

Majalisar Dokokin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) shiyar Sokoto ta gargadi mambobinta kan hada baki da ‘yan siyasa a zaben 2023 mai zuwa.

Kamfanin Dillancin Labaran kasa NAN ya rawaito cewa, an yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a karshen taronta da shugaban kungiyar ta NUJ ta jihar da Sakatarensa Dalhatu Safial-Magori da Muhammad Bello suka sanya wa hannu.

An gargadi ’yan jarida kada su bari ayi amfani da su wajen zage-zage da jagaliya don samun tagomashin da bai dace ba daga ‘yan siyasa.

 “Yayin da babban zaben 2023 ke gabatowa, ya kamata mambobin su ci gaba da kasancewa masu rike amanar Al'umma ta hanyar tabbatar da gaskiya, rungumar kowa da yin aiki da kwarewa.

Don haka ana gargadin mambobin kungiyar, cewa kungiyar ba zata tsayawa duk wanda ya saba wa ka’ida da gangan don cin mutuncin kansa ba, ”in ji ta.

Kungiyar ta kuma roki ‘yan siyasa da su tabbatar da an gudanar da yakin neman zabe cikin lumana. Haka kuma ta bukaci gwamnatocin tarayya da na Sokoto da su bullo da hanyoyin da za a bi domin tunkarar kalubalen tsaro a jihar da kuma kasa baki daya.

 “Ya kamata gwamnati ta gaggauta daukar matakai domin tunkarar kalubalen kaura zuwa birane, karuwar yawan barace-barace a kan tituna da kuma kara yawan ‘yan gudun hijirar saboda tsananin rashin tsaro a kasar nan.

 Sanarwar ta kuma bukaci Gwamnatin jihar Sokoto, ta gaggauta kafa wata ma'aikata ko hukumar 'yan gudun hijira da za ta taimaka wajen dakile karuwar masu bara a titunan jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci