OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Dan sanda da jami'an CJTF 5 da aka sace sun tsere daga Boko Haram a Borno

Dan sanda da jami'an CJTF 5 da aka sace sun tsere daga Boko

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da tserewar wasu jami’an tsaro shida da ‘yan ta’addar ISWAP suka yi garkuwa da su a Benishek ranar Litinin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da ya yi da jami’an ‘yan sanda reshen jihar a ranar Laraba a Maiduguri.

“Yan ta’addan sun yi awon gaba da jami’an tsaro shida da suka hada da dan sanda daya, jam'ian Civilian joint Task Force uku da mafarauta uku.

“Sun kuma kwace motar sintiri kirar Hilux guda daya sannan sun kuma sun kwace bindiga kirar AK 47 guda daya.

"Tare da taimakon rundunar sojin sama, jami'an tsaron sun samu nasarar tserewa bayan da maharan sun kutsa cikin daji a lokacin da suka hangi Sojojin" in ji shi.

Sai dai kwamishinan 'yan sandan ya ce 'yan ta'addan sun kashe mutane uku tare da kona motoci 4 da kuma ofishin jami'an Rapid Response Squad a harin da suka kai a Benisheik.

Mista Umar ya ce ‘yan ta’addan sun kutsa cikin garin ne da misalin karfe 3 na safiyar ranar Litinin inda suka auka wa rundunar Civilian Joint Task Force, CJTF.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci