OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NEMA Ta Karbi ‘Yan Najeriya 542 Da Aka Dawo Dasu Daga UAE

Hukumar NEMA Ta Karbi ‘Yan Najeriya 542 Da Aka Dawo Dasu D

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta karbi ‘yan Najeriya 542 daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

 Manzo Ezekiel, shugaban sashin yada labarai na NEMA, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi a Abuja.

 A cewarsa, wadanda suka dawo sun isa filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja a cikin jirgin Max Air da karfe 4:29 na safe.

 Ya kara da cewa wadanda suka dawo sun hada da maza 79, mata 460 da jarirai uku.

Ya kara da cewa jami’an kiwon lafiya sun tantance mutanen da suka dawo, sannan hukumar shige da fice ta Najeriya ta tantance su daga bisani Kuma NEMA ta basu kudin motar da zai taimaka musu komawa gidajen su.

 Tun da farko, MMustapha Ahmed, Darakta-Janar na NEMA, wanda ya karbi mutanen da suka dawo a hukumance a madadin Gwamnatin Tarayya, ya gargade su da su yi koyi da abubuwan da suka faru kuma su kasance masu bin doka da oda.

 Ahmed, wanda ya samu wakilcin Daraktan Kudi da Akanta na Hukumar, Mista Sani Jiba, ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da dawo dasu Najeriya kafin tallafa musu komawa gidajensu.

 Jakadan Najeriya a Dubai, Amb. Atinuke Mohammed, wanda ya raka mutanen da suka dawo kasar, ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan sa baki na musamman wajen kwashe ‘yan kasar cikin koshin lafiya.

 Jami’an NEMA da jami’an filin jirgin sama da jami’an tsaro da hukumar ‘yan gudun hijira ta kasa (NCFRMI), NAPTIP, NIDCOM, NDLEA da dai sauransu ne suka tarbi wadanda suka dawo.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci