OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ambaliyar Ruwa: Sama Da Mutane 20 Sun Rasa Rayukan Su, 116,084 Sun Rasa Matsuguni A Benue

Ambaliyar Ruwa: Sama Da Mutane 20 Sun Rasa Rayukan Su,  116,

Wasu da ambaliyar ruwa ya shafa a bana

Akalla mutane 23 ne aka ruwaito sun mutu, wasu 116,084 kuma suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Benue.

Sakataren zartarwa na Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Benue (SEMA), Emmanuel Shior, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wani taron manema labarai a Makurdi don kaddamar da rabon kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.

Ya bayyana cewa an samu mace-mace 14 a karamar hukumar Guma, biyu a karamar hukumar Vandekiya, hudu a karamar hukumar Katsina-Ala da uku a karamar hukumar Agatu.

 Shior ya ci gaba da bayyana cewa adadin gonaki mai fadin hekta 14,040 ne ambaliyar ruwa ta rutsa da su yayin da gidaje 4,411 suka nutse a yanzu.

Ya ce an samar wa da wadanda suka rasa muhallansu 116,084  gidaje 12,856 a kananan hukumomi 11 a yankuna 104 da abin ya shafa sannan kuma mutum14 sun  jikkata.

Ya kuma ce hukumar za ta kwashe mutanen da suka rasa matsugunansu a Agatu da suka mamaye babbar hanyar zuwa wani sansani da aka kebe inda za a samar musu da kayan agaji da tsaro.

Ya lissafa kananan hukumomin guda 11 da suka hada da Guma, Vandekiya, Otukpo, Kastina-Ala, Makurdi, Apa, Agatu, Tarka, Gboko, Gwer West da Logo, inda ya jaddada cewa Makurdi da Agatu ne ambaliyar ta fi shafa.

Da yake jawabin, babban jami’in hukumar NEMA mai kula da bincike da ceto Digha John, ya bayyana cewa a cikin jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar nan a bana, Borno, Benue da Kogi ne suka fi fama da matsalar.

John ya ce, saboda haka hukumar NEMA ta tura motarta na tace ruwa a cikin gaggawa domin tsaftace gurbataccen ruwan da kuma rarrabawa al’ummomin da abin ya shafa a jihar Benue.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai