OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamna Wike Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan Guda Domin Tallafawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Rutsa Da Su

Gwamna Wike Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan Guda Domin Tall

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya amince da kashe Naira biliyan 1 don daukar matakan gaggawa da tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin Ahoada ta yamma,Ogba,Egbema, da Ndoni na jihar.

Gwamna Wike, ya amince da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal a ranar Larabar da ta gabata.

Ya tabbatar da cewar gwamnatin jihar Ribas ta amince da kudaden don baiwa marasa galihu dama, musamman a kananan hukumomin Ahoada ta Yamma da Ogba, Egbema da Ndoni wadanda su ne yankunan da ambaliyar ruwan tafi yiwa barna a jihar 

Hakazalika, za'a yi amfani da kudin wajen gyara barnar da ambaliyar ruwa, wanda ya shafi gidaje, gonaki tare da tilasta mazauna yankin yin ƙaura.

Gwamnan wanda ya jajanta wa wadanda ambaliyar ta shafa, ya kuma kafa wata kungiya mai zaman kanta da za ta tsara yadda za a raba kayan agaji ga al’ummomin da abin ya shafa a jihar.

Ambaliyar ruwa de a damunar bana tayi sanadiyar rasa rayuka, ta kuma shafe kauyuka da dama, gonaki, hadi da raba dubban al'umma da mazaunin su a fadin kasar nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci