OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Diyar Sanata Ekweremedu Ta Nemi Jama'a Sun Tallafa Mata Da Koda

Diyar Sanata Ekweremedu Ta Nemi Jama'a Sun Tallafa Mata Da

Sonia Ekweremadu, diyar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, ta bukaci jama’a da su taimaka su ba ta gudummawar koda.

Ms Sonia, wacce a halin yanzu iyayenta ke fuskantar tuhumar girbin sassan jiki a Burtaniya, ta yi wannan roko ne ta shafin ta na Instagram @soniaekw ranar Litinin.

A cewarta, ta daina zuwa makaranta inda take karatun digiri na biyu tun shekarar 2019 bayan da aka gano tana fama da cutar koda.

Yayin da take neman taimako, Ms Sonia ta bayyana cewa ikon Allah ne kawai ya sa take raye har yanzu, ta kara da cewa ana mata wankin koda na tsawon Awa biyar sau uku a kowani sati.

Ta kuma bayyana cewa halin da iyayenta ke ciki ya kara dagula al'amura a halin yanzu.

Ga abinda Sanarwar ta ce :“Ni Sonia Ekweremadu, ina kira ga jama’a da su kawo min agaji domin ceto rayuwata.

"Iyali na sun yi kokari don ceton rai na kuma sun kai ni asibitoci daban-daban, amma ciwon ya ci gaba da ci na.

“Ikon Allah ne kawai yasa nake raye har yanzu A halin yanzu ina London, ina karbar wankin koda duk bayan sa'o'i biyar sau uku ko hudu a kowani mako.

“Shekaru ukun da suka gabata sun kasance masu matukar wahala.

"Tuhumar da iyayena ke fuskanta a Landan a halin yanzu yana da alaka ne da rashin lafiya ta.

“Bana so ince komai game da wannan lamari saboda har yanzu maganar tana gaban kotu kuma nasan cewa gaskiya zatayi halin ta.

"Duk wanda yaga wannan roko nawa kuma yanada niyyar taimaka min da gudummawar kodar sa ya na iya aiko da imel zuwa [email protected]  kuma ya haɗa da sunansa, lambar waya, adireshin imel da wurin zama."

Jim kadan bayan sakin wannan sako an sami Wata mata ‘yar garin Ilorin mai suna Martha Uche ta bayyana cewa a shirye ta ke ta ba da gudummawar kodarta domin ceto rayuwar diyar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Ga abinda ta ce:"Ina so in taimaka mata in ba ta koda ta daya, ina so in taimake ta domin na riga na ganta kuma an nuna min a mafarki." 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci