OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Tarayya ta dauki lauyoyin da za su kare Ekweremadu a kasar Birtaniya

Gwamnatin Tarayya ta dauki lauyoyin da za su kare Ekweremadu

Gwamnatin tarayya ta dauki wasu lauyoyi da za su tsaya wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu a kasar Birtaniya kan batun cire sassan jikin mutum ba bisa ka'ida ba. 

An kama Ekweremadu da matar sa ​​Beatrice a makon da ta gabata.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan wani zaman da majalisar ta yi a sirrance. 

Lawan ya ce majalisar dattawan ta kafa wata tawaga da za ta ziyarci tsohon shugaban majalisar dattawan a Landan ranar 1 ga watan Yuli, 2022.

Idan dai za a iya tunawa, bayan kama Ekweremadu da matar sa, wata kotun majistare a birnin Landan ta yanke hukuncin a tsare su ​​a hannun 'yan sanda har zuwa ranar 7 ga watan Yuli domin ci gaba da sauraron karar.

Da yake bayyana wadanda za su ziyarci Ekweremadu, Lawan ya ce kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje zai bar kasar zuwa Landan a karkashin jagorancin Sanata Adamu Bulkachuwa.

Ya kuma bayyana cewa majalisar dattawa za ta hada kai da babbar hukumar Najeriya da ke Landan da ma’aikatar harkokin wajen kasar domin kwato masa ‘yancin sa.

Lawan ya bayyana cewa, “Na yi ganawar sirri da babban kwamishinan mu na Najeriya a kasar Biritaniya, Alhaji Isola Sarafa, wanda ya yi matukar kokari wajen kulla alaka da abokin aikinmu, wanda ya samu nasarar shigar da tawagarsa a kotu a Uxbridge inda a can aka kai Ekweremadu.

“Muna yaba musu bisa yadda suka ba da hankali kan lamarin da ke faruwa.

"Hakazalika, Ministan Harkokin Wajen Najeriya yana kokari domin ma'aikatar harkokin wajen ta dauki matakan ba da goyon bayan diflomasiyya ga abokin aikinmu."

Ya kuma kara nanata kudurin majalisar dattawa na tabbatar da ‘yancin Ekweremadu. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai