OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Da Dumi-Dumi: Sakataren Riko na Jam’iyyar APC, Akpanudoedehe, Yayi Murabus

Da Dumi-Dumi: Sakataren Riko na Jam’iyyar APC, Akpanudoede

Sakataren kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya yi murabus.

Duk da cewa ba a bayyana dalilan murabus din nasa ba, amma ba za a raba shi da rigingimun da ke faruwa a jam’iyyar ba.

Tuni dai sakataren ya fice daga sakatariyar jam’iyyar ta kasa da dukkan kayan sa kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jam’iyyar ta shirya gudanar da babban taron ta na kasa a ranar 26 ga watan Maris na 2022 a Abuja.

Haka kuma an yi ta cece-kuce game da shugabancin jam’iyyar har zuwa ranar Litinin 7 ga watan Maris na 2022.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci