OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Civilian JTF sun dakile wani hari a Katsina, sun kashe 'yan bindiga 9

Civilian JTF sun dakile wani hari a Katsina, sun kashe 'yan

Rundunar Civilian Joint Task Force (CJTF) a jihar Katsina ta dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Batsari da ke jihar.

A yayin harin, rundunar ta CJTF ta samu nasarar kawar da maharan tara tare da kama wasu biyar.

Leadership ta ruwaito cewa wata majiya mai tushe ta bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi yayin da suke kan babura goma tare da rike da manyan makamai.

Majiyar ta kara da cewa maharan sun yi arangama da jami’an CJTF da suka dakile harin.

Rundunar ta kuma kwato babura tara daga cikin goman da maharan suka zo da su. 

A cewar rahoto, an kai hari garin kwanan nan wanda ya kai ga sace wasu mutane.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da ke addabar al’umma.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci