OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

CISLAC Ta Gargadi Gwamnoni Kan Bawa Jami'an Tsaro Na Wucin Gadi Makamai

CISLAC Ta Gargadi Gwamnoni Kan Bawa Jami'an Tsaro Na Wucin G

Wta kungiya mai rajin karen dokokin tsarin mulki, mai suna Civil Society Legislative Advocacy Centre, CISLAC, ya nuna rashin goyon baya ga tsarin wasu gwamnatocin jihohi na kirkirar jami'an wucin gadi da basu makamai don yaki da yan ta'adda dake kai hare-hare a jihohin su.

Shugaban ƙungiyar, Auwal Ibrahim Musa, ya bayyana haka ne a yayin jawabin sa a gurin taron wakar da kai da aka shiryawa yan jarida a birnin Legas.

"A maimakon zartar da hukunci da yaci karo da kundin dokokin kasar nan, kamata ya yi gwamnonin su nemi yan majalisar wakilai dake wakilitar sassan jihohin su a zauren majalisar dokokin kasa da su kai kudirin gyara samar da doka da zata ba damar kirkirar yan sanda a jihohin su.

"Bayar da makamai ga wasu jami'ai da basu da gurbi a kundin tsarin mulki kuskure ne da zai iya kara ta'azzara lalacewar tsaro a Najeriya.

Musa ya kara da cewa, daga shekarar 2015 kawo yanzu an kashe tiriliyoyin Naira wajen inganta fannin tsaro, amma an rasa rayuka da dama sakamakon ci gaba da hare-haren ba ƙaƙƙautawa.

Shugaban kungiyar ta CISLAC, ya kuma nuna damuwa kan yaduwar kananan makamai, in da ya shawarci yan jaridu da su mai da hankali kan yin bincike tare da yada ayyukan hukumar shige da fice domin taimakawa wajen rage fasakorin munanan abubuwa zuwa cikin kasar nan.

Daga karshe, Musa yace, "gwanonin na da damar bukatar sauye-sauye kan dokoki da suka shafi fannin tsaro domin yin amafani da tsare tsaren su na kawo karshen matsalar rashin zan lafiya a fadin jihohin su."

 

TN

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci