OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Borno: Zulum Ya Amince Da Tallafin N50m Ga Dalibai 2,019

Borno: Zulum Ya Amince Da Tallafin N50m Ga Dalibai 2,019

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da tallafin naira miliyan 50 ga dalibai 2,019 na Ramat Polytechnic.

An ba da tallafin ne don biyan kudin rajistar ɗalibai don zaman karatun na zangon 2021/2022.

Sakataren zartarwa na hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno, Malam Bala Isa ne ya bayyana hakan a yau (Litinin).

A cewar sa, amincewar gwamnan don tallafawa ci gaban ‘yan asalin jihar ne.

Isa ya ce hukumar za ta ajiye batun biyan kudin tallafin karatu ga Jami’o’in Tarayya har sai lokacin da kungiyar ASUU ta janye yajin aiki.

Daga karshe ya yabawa gwamnan bisa wannan karimcin da ya nuna yayin da ya bukaci daliban da su zamto wanda jihar zata yi alfahari da su. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci