OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: Tambuwal Ya Dakatar Da Albashin Malaman Jami'ar Jihar Sakkwato

ASUU: Tambuwal Ya Dakatar Da Albashin Malaman Jami'ar Jihar

Gwamna Aminu Tambuwal

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya dakatar da albashin malaman jami'ar Jihar Sakkwato da ke yajin aiki.

Tambuwal ya bayyana haka ne da da yake zantawa da matasa a cibiyar taron ƙasa da ƙasa da ke gudana.

Gwamnan yace yana alfahari da biyan malaman har na tsawon sama da wata biyar ba tare da yin wani aiki ba.

 “A watan da ya gabata, na dakatar da biyan albashin ma’aikata, saboda na yi alfahari da biyan su albashin sama da watanni biyar ba tare da aiki ba.

“Na nemi su koma bakin aiki ko kuma su haƙura da albashin su, saboda ba su da wani dalilin ci gaba da yajin aikin.

“Batun da rassan ASUU a jami’o’in tarayya suka gabatar ba ɗaya suke da abin da ake samu a jami’o'in jihohi ba. 

"Idan kuma suna da wasu batutuwa ko ƙorafi su fito da su, in ba haka ba, ba za mu biya su albashi ba har sai sun koma aiki,” inji shi.

A ƙarshe ya shawarci malaman da su koma bakin aiki idan da gaske suna da muradin cigaban jihar da ɗaliban ta a zuciyar su.

Ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta fara yajin aikin a watan Fabrairu saboda buƙatar inganta walwala da sauran su, cewar Jaridar Daily Trust.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci