OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU : Kotu ta umarci ASUU da ta janye yajin aikin

ASUU : Kotu ta umarci ASUU da ta janye yajin aikin

A yau Laraba ne kotun masana’antu ta Najeriya ta umarci kungiyar malaman jami’o’i da ta janye yajin aikin da ta shafe watanni tana yi .

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ASUU ta tsunduma yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu domin neman a biya su hakkokin su da suka hada da inganta jami’o’i, nazarin albashin malaman jami’o’i da dai sauransu.

An yi ta zaman ganawa tsakanin gwamnati da Mambobin kungiyar ta ASUU sai dai har yanzu an kasa cimma matsaya.

Sakamakon haka gwamnatin tarayya ta garzaya kotu domin kalubalantar yajin aikin.

Kamar yadda shafin jaridar TheCable ya ruwaito, gwamnatin ta bakin lauyanta, James Igwe, ya roki kotun da ta dakatar da ASUU daga cigaba da yajin aikin, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci