OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Basaraken Gargajiya Da Matarsa A Kwara

Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Basaraken Gargajiya Da Matarsa

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da basaraken gargajiyar Owa-Onire da ke gundumar sanata ta Kudu a jihar Kwara tare da matar sa.

Rahotanni ya bayyana cewa an tafi da sarkin ne tare da matarsa ​​da direbansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Okasanmi Ajayi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

Ya bayyana cewa mutane biyun da ake zargin suna hannun ƴan sanda kuma an ceto matar sarkin gargajiyar.

Yayin da ya tabbatar wa jama'a cewa rundunar su zasu ci gaba da kokarin kwato sauran mutanen.

Okasanmi ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Paul Odama ya aike da tawagar masu bincike.

A cewarsa, za a bayyana cikakken rahoto kan lamarin da zarar an kammala bincike.

Najeria na fama da haren-haren ƴan bindiga musamman a yankunan Arewa maso yamma da ta tsakiya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci